ABNA24 : A cikin wani sako da ya buga a shafinsa na Twitter, firayi ministan Khan, ya kirayi shugabannin kasashen musulmi da su hada hannayensu da karfin su waje guda wajen fada da wannan annobar ta kyamar Musulunci da ke yawo a kasashen Turai.
A cikin wasikar tasa, firayi ministan na Pakistan ya ce: maganganun baya-bayan nan da suka fito daga bangaren wani shugaba wani lamari ne da ke nuni da irin yaduwar kyamar Musulunci da kiyayya da shi da ke ci gaba da yaduwa a kasashen Turai inda musulmi ‘yan tsiraru suke rayu.
Firayi minista Khan ya ce wadannan shugabanni na Turai ba su fahimci irin so da kaunar da Musulumi a duk fadin duniya suke wa Annabi (s.a.w.a) da kuma Littafinsu mai tsarki, Alkur’ani mai girma, wanda ya ce irin abubwan da suke aikatawa ne ya ke haifar da irin martani mai kaushi da ke faruwa a halin yanzu.
Wannan dai ba shi karon farko da firayi ministan na Pakistan yake magana kan irin wannan danyen aiki na cin zarafin Annabi (s.a.w.a) da ake yi a kasar Faransa wanda kuma shugaban kasar Emmanuel Macron ya goyi baya lamarin da ke ci gaba da janyo masa tofin Allah a duniyar musulmin.
342/